On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

An Haramta Yin Amfani Da TikTok A Amurika

Majalisar dattawan Amurika ta amince da kudirin dokar nan da ake cece kuce kansa na haramta yin amfani da shafin TikTok.

Majalisar  ta baiwa mai kamfanin dan kasar China  Byete Dance wa’adin watanni tara  da  ya  siyar hajojinsa   dake kan shafi ko kuma a kulle shi baki  daya a kasar ta Amurika.

A yanzu an mika kudirin dokar ga shugaba Joe Biden wanda  y ace zai rattaba mata hannu da zarar ta  riski teburinsa na shugaban kasa.

Idan har Amurika ta samu nasara wajen tilasta mai kanfanin na TikTok siyar  das hi, hakan zai sa  duk wata yarjejeniya da za’a yi dole ne sai da amincewar kasar China, kuma kasar ta  lashi takobin sukar  matakin.