On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

EFCC Na Tuhumar Emefiele Da Bada Kwangilar Buga Kudi Akan Sama Da Naira Bilyan 18

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta sake kai karar tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefeile kara a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja.

A sabuwar tuhumar, Hukumar  na zargin Emefiele  da amincewa  a buga takarduna kudi na milyan 684 da dubu 590 akan kudi naira bilyan 18 da milyan 96.

Hukumar ta EFCC ta zargi  tsohon gwamnan  da  karya doka  domin cutar da jama’ar kasa  a  yayin aiwatar  da shirinsa  na canjin kudi a zamanin  tsohon shugaban kasa  Muhammadu Buhari.

Hukumar  ta  zargi  Emefiele  da cire tsabar kudi naira  bilyan 124 da  milyan 800 daga cikin asusun tattara  haraji  na kasa.

Babban mai gabatar da kara na hukumar EFCC,  Lauya Rotimi Oyedepo SAN, ya  ce za’a gurfanar da Emefiele gaban mai shari’a Hamza Mu’azu kan sabbin tuhume-tuhume guda hudu, wanda suka shafi rashin yin biyayya ga doka, da buga kudi  ta haramtacciyar  hanya da sauran lefuka.