On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Tarayya Ta Karbo Sama Da Naira Bilyan 57 Daga Cikin Bashin Da Take Bin Mutane Da kanfanoni

Gwamnatin tarayya ta sanar da karbo wasu kudade hara naira milyan dubu 57 daga cikin naira tiriliyan 5 da bilyan 5 da hukumar tattara kudaden shiga ta kasa da sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya ke bin bashi.

Babban sakatare aiyuka  na musamman  a   ma’aikatar kudi ta kas  a Okokon Ekanem Udo  ne ya baiyana haka jiya a Enugu a  yayin wani taron karawa  juna  sani, kan   gano  bashin da gwamnatin tarayya ke bi.

Ya  ce an gano kudaden  daga hannun wadanda ake bin bashi sama da mutane dubu 5 a karkashin ma’aikatun gwamnati sama da  93.

Ya  ce  bayanan da suke da  shi sun nuna cewar  mafi yawa daga cikin kanfanoni da daidaikun mutane  da  suka ki biyan bashin da gwamnatin ke binsu, a halin yanzu sun fara biyan bashin.