On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Kungiyar FIDAC Ta Koka Kan Matsalar Karancin Ruwan Sha A Kano

Wata kungiyar kungiyar farar hula mai suna FIDA, ta bukaci gwamnatin jihar Kano data aiyana dokar ta baci a bangaren samar da ruwan sha a jihar Kano.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir  Yusuf  da  ya  gaggauta amincewa  da fitar da kudi  domin magance matsalar karancin ruwan sha  da ake fuskanta.

A wata sanarwa da  shugaban kungiyar  Dr. Abdussalam Muhammad Kani  ya fitar  a jiya, Ya  bukaci  gwamnatin jihar kano  data  gyara  daukacin kayayyakin samar da ruwa da ake das u  domin samar da wadatuwarsa  a  birni  da  karkara.

Idan ba’a manta ba a kwanan nan ne  Hukumar  samar da ruwan sha  ta jihar  kano ta yi karin haske kan dalilan da suka sabbaba matsalar karancin ruwan sha, wanda ta  ce  yana da alaka  da gyare-gyaren da ake yi a challawa da Tamburawa, A yayin da  ‘yan garuwa suka kara kudin ruwa daga naira  50 zuwa 150 akan kowacce  jarka daya a sassa daban daban na kwaryar  birnin kano.