On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Wani Matashi Ya Rataye Kansa A Karamar Hukumar Bebeji Ta Jihar Kano

Wani matashi mai kimanin shekaru goma sha - shida da haihuwa mai suna Ibrahim Lawan ya rataye kansa a kauyen Kuki dake Karamar hukumar Bebeji ta nan jihar Kano dake karkashi ikon masarautar Rano.

Jami'in yada labarai na masarautar Nasiru Habu Faragai   Shine ya  tabbatar da haka  ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Arewa Radiyo.
 

Sanarwar  ta  baiyana cewa   Hakimin Bebeji Maji Dadin Rano, Alhaji Tijjani Abdullahi Kuki ya gabatarwa mai Martaba Sarkin Rano, Ambassador kabiru Muhammad Inuwa rahoton faruwar lamarin, Wanda  ya faru a ranar sha - hudu ga watan Ogusta da muke ciki, inda  aka tarar da matashin ya Rigamu Gidan Gaskiya.

  Mai Martaba Sarkin Rano  ya bukaci a mika rahoton ga jami'an  'Yan sanda domin fadada bincike.

 Haka Zalika an gabatarwa da Sarkin rahoton mutuwar wani Dan  achaba Mai suna Abdullahi Isa   wanda aka fi sani da   Tambai  dake kauyen Kodai Chirin  a yankin karamar hukumar Bunkure, wanda aka same shi Yashe a gefen hanya an cire masa hannu sannan  kuma an yi awun gaba da babur dinsa.

  Da yake karbar rahoton, Mai Martaba Sarkin Rano, ya bukaci Hakimai da Dagatai da masu  Unguwanni dake masarautar dasu tashi  tsaye wajen gudanar da addu'oi domin neman daukin Allah Madaukakin sarki  daga  samun faruwar irin wadannan matsaloli.