On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Amaju Pininck na fuskantar matsin lamba

Rashin nasarar da kungiyar Super Eagles tayi bai yi wa...

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa NFF Mr Amaju Melvin Pinnick yana fuskantar matsin lamba daga masu ruwa da tsaki a bangaren kwallon kafa a Najeriya wadanda suka bukaci ya sauka daga mukamin sa ba tare da bata lokaci ba, biyo bayan gazawar da Najeriya tayi na samun gurbin buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 da za’a gudanar a kasar Qatar.

Rashin nasarar da kungiyar Super Eagles tayi bai yi wa miliyoyin 'yan Najeriya dadi ba, ciki harda  shugaban kasa Mumammad Buhari, wanda ya ziyarci filin wasa na Moshood Abiola dake Abuja domin baiwa kungiyar kwarin gwiwa.  

Bayan rashin nasarar ne masu ruwa da tsaki a bangaren kwallon kafa suka yi kira ga shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa NFF Pinick da tawagar sa dasu sauka daga kan mukaman su ba tare da bata lokaci ba, a yayin da suka dora alhakin rashin nasarar da super eagles tayi akan rashin jagoranci mai kyau a hukumar NFF.