On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Najeriya Za Su Ci Gaba Da Amfani Da Takardun Takardun Kudinsu Inji Tinubu

Shugaban kasar ya baiyana haka ne ta cikin jawabinsa da ya gabatar a dandalin taro na Eagle Square dake Abuja babban birnin taraiyya.

A cewarsa  tsarin sauyin takardun kudin da babban bankin kasa  ya bijiro dashi   ya yi matukar kuntatawa jama’ar  kasa.

Ya kuma baiyana cewar  a yayin da gwamnatinsa  zata yi gyara kan tsarin,  jama’a  zasu cigaba da amfani da  takardun kudin  ba tare da samun wata matsala ba.

Bugu da kari ya  ce za’a yi sauye-sauye  kan tsarin  tafiyar da manufofin kudi na kasa.