On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Abba Kabir Yusif Ya Zama Zababben Gwamnan Jihar Kano A Jam'iyyar NNPP

An ayyana dan takarar NNPP, Abba Kabiru Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

Jami’in tattara sakamakon zabe na jihar, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim shine ya bayyana hakan da safiyar yau, inda ya ce Abba Kabir Yusuf ya lashe kananan hukumomi 30 daga cikin kananan hukumomi 44 da ya samu kuri’u milliyan 1 da dubu 19 da 602.

Abokin takararsa na jam’iyyar, APC Dr Nasiru Yusif Gawuna ya  samu kuri’u dubu 890 da 705 bayan ta lashe sauran kananan hukumomi 14.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Kano tana da mutane milliyan 5 da dubu  921 da 370 da suka yi rijistar zabe, daga cikinsu mutane milliyan  2 da dubu 32 da 955 ne aka tantance a zaben gwamna.

Sakamakon ya nuna cewa jimillar kuri'un da aka kada sun kai miliyan 2 da dubu 4 da 964.