Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi Allah wadai da aikin rusau da gwamnatin jam’iyyar NNPP ke gudanarwa a jihar Kano, wanda ta baiyana amatsayin rusa tattalin arziki.
An samu bayyanar wakilai biyu dake ikirarin samun kujerar jagorantar majalisar dokoki ta 7 a jihar Nasarawa.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta amince da jerin sunayen ‘yan takara na karshe na zaben gwamna da za’a gudanar a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Mukaddashin Manajan Darakta na sabon Kamfanin Jiragen sama na Najeriya, Kaftin Dapo Olumide, yace jirgin da ya yi batan dabo dauke da tambarin jirgin Najeriya Air Airline an yi hayarsa ne daga Kamfanin Jiragen Sama na Habasha domin kaddamar da tambarin.
Majalisar Wakilai ta ayyana kaddamar da kamfanin na Nigeria Air amatsayin yaudara bayan da manyan masu ruwa da tsaki a cikin yarjejeniyar suka musanta labarin kaddamar da jirgin.
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta dakatar da shirin tafiya yajin aikin da ta tsara farawa daga gobe Laraba kan karin farashin man fetur sakamakon cire tallafin da ta yi.
Kungiyar kwadago ta TUC tayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kara mafi karancin albashin ma’aikata a kasarnan zuwa Naira dubu 200 domin dakile illolin cire tallafin man Fetur.
Farashin man jiragen sama da aka fi sani da Jet A1 ya sauka jim kadan bayan an cire tallafin mai wanda ya yi tashin gwauron zaɓi.
Shugaban ma’aikatan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ibrahim Gambari, ya mikawa kakakin majalisar wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, ragamar aiki.
A rana irin ta yau 6 ga watan Yuni na shekarar 2014 Allah ya yiwa sarkin na 13 a daular Fulani rasuwa yana da shekara 84.
kungiyar dillalan man fetur ta kasa mai zaman kanta IPMAN, ta ce sabon farashin Litar man fetur ba zai iya kasa da naira 500 ba.
Gabanin bikin ranar hawa Keke ta duniya da ake yi duk ranar 3 ga watan Yunin kowacce shekara, kungiyar masu hawa kekuna ta duniya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kudaden tallafin mai wajen inganta harkar sufurin hawan keke wanda hakan zai temaka wajen dakile matsalar sufuri da tallafin cire tallafin man ya haifar.
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain PSG Christophe Galtier ya tabbatar da ficewar Dan wasa Lionel Messi daga kungiyar, Inda ya yi fatan magoya bayan kungiyar za su yi masa bankwana na musamman wasansa na karshe da kungiyar zata buga a ranar Asabar.
Shugaba Joe Biden ya fadi akan wani dandamalin gabatar da jawabi a yayin wani taro da aka gabatar a Kwalejin horas da Sojojin Sama da ke Colorado, sai dai rahotanni sun baiyana cewar bai ji wani ciwo ba.
Kanfanin sarrafa Albarkatun mai na kasa NNPCL, Ya baiyana cewar matatar mai ta Dangote da ta Fatakwal da kuma sauran wadanda ake dasu, ba zasu sa a samu sauyin farashin man fetir ba.
Kugiyar Kwadago ta NLC ta musanta wasu rahotanni dake baiyana cewar, tana shirin fara yajin aiki daga yau, saboda janye tallafin mai da gwamnatin taraiyya ta yi.
ata kungiya mai zaman kanta, dake rajin yaki da rashin adalci, War against Injusice, Ta bukaci hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, data kama tare kuma da yin bincike sannan kuma ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje gaban kotu, saboda zarginsa da aikata almundahanar Dala Milyan Biyar.
Gwamnan jihar kano, Alhaji Abba Kabir Yusif ya amince da yin karin wasu sabbin nade-nade har guda biyar, akan wasu mukamai daban-daban, a yayin da za’a yi bukin rantsar da mutanen nan bada jimawa ba.
An tashi batare da cimma wata matsaya ba a ganawar da aka yi tsakanin Gamaiyyar kungiyoyin kwadago na kasar nan, da kuma wakilan gwamnatin taraiyya kan batun cire tallafin mai, a daren jiya.
Wasu rahotanni na baiyana cewar takarar da tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ke yi na zama shugaban majalisar dattawa ta gamu da cikas, yayin da wata majiya ta baiyana cewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye goyon bayan da yake yi masa.
Sanata Ibrahim Shekarau dake wakiltar Kano ta tsakiya, ya koka kan makudan kudin da ake kashewa da sunan tafiyar da al’amuran gwamnati, inda ya shawarci shugaba Bola Tinubu kan bukatar rage yawan ‘yan majalisar dokokin taraiyya da ake dasu.
Wani rahoton hadin gwiwa da shirin bunkasa samar da Abinci na Duniya da kuma Hukumar samar da Abinci da bunkasa aikin gona ta Majalisar dinkin duniya suka fitar, ya ce sama da ‘yan Najeriya miliyan 24 da dubu dari 8 na fuskantar barazanar karancin abinci tsakanin watan Yuni da Agusta.
Kungiyar Kwadago ta NLC ta gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya kuntatawa ‘yan Najeriya biyo bayan kalamansa da ya yi kan cire tallafin man fetur, wanda hakan ya fara haifar da matsalar karancinsa a yanzu haka.
To a wani mataki na gaggawa da aka dauka domin shawo kan matsalar ta Man fetir, Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da shugaban kanfanin mai na kasa NNPC, Mele Kyari da gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele da sauran manyan mukarraban gamnati a fadar shugaban kasa a ranar Talata.
Farashin man fetur ya karu zuwa Naira Dubu 1 da 200 kan kowace lita a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a jiya, Tun bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya aiyana cire tallafin mai.
Ana danganta dan wasan Brazil Neymar da komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester city mai buga gasar zakarun Premier
Shugaban kasar ya baiyana haka ne ta cikin jawabinsa da ya gabatar a dandalin taro na Eagle Square dake Abuja babban birnin taraiyya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Ya amince da nada sabon babban sakataren hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, tare da jami’ar gudanarwar hukumar.
Shugaban kasar Amurika,Joe Biden ya yi alkawarin yin aiki tare da sabon shugaban kasa, Bola Tinubu ta fannin inganta tattalin arziki da kuma sha’anin tsaro.
‘Yan sa’oi bayan sanarwar da sabon shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yi na cewar biyan tallafin mai ya zama tarihi a kasar nan, a yanzu haka an fara samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai dake Abuja da Legas da kuma wasu jihohin kasar nan.
Sabon gwamnan jihar Kano,Ya bada umarnin cewar daga ranar 1 ga watan gobe na Yuni,Ya zama wajibi dukkanin wasu motoci dake bin titinan jihar kano da kuma Shagunan siyar da kayayyaki, su kasance suna da kwandon zuba shara a wurarensu, domin tabbatar da tsaftace jihar kano.
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da nadin mukaman farko a gwamnatinsa.
Audio
Yayin da wasu matasa a Najeriya ke bata lokacinsu dake da muhimmanci wajen yin nishadi a shafukan sada zumunta, tunanin ya sha bambam ga wani matashi a hukumar Dambatta ta jihar Kano.
Bayan kammala wa'adin shekara 8 Muhammadu Buhari ya zama tsohon shugaban Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki amatsayin sabon shugaban kasar Najeriya na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Uwargidan zababben shugaban kasa, Remi Tinubu, ta ce Allah ya sanya Albarka ga iyalanta, kuma ba sa bukatar dukiya ko arzikin Najeriya domin rayuwa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin babban sakataren zartaswa na hukumar kula da Almajiri da ilimin yaran da ba sa zuwa makaranta.
Majalisar tsaro ta jihar Kano ta ayyana satar waya a matsayin fashi da makami, kuma duk wani mutum ko kungiya da aka kama da aikata laifin za su fuskanci hukuncin hakan.
Babban Sufeton rundunar ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin mayar da jami’an ‘yan sanda uku bakin aikinsu biyo bayan korarsu, a watannin baya sakamakon amfani da bindiga ba bisa ka’ida ba.
Shugaban Kasa Muhammadu Bihari, ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya.
Kotun Kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka daukaka a gabanta dake neman a soke cancantar takarar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shattima na jam'iyyar APC.
An hango wani jirgin saman Nigeria Air a filin jirgin saman Addis Ababa Bole dake kasar Habasha.
Jirgin dauke da maniyata 472 daga jihar Nassarawa da jami'ai 27 ya sauka a filin jirgin saman Muhammad Ibn Abdu-Azeez dake Madina da karfe 3:20 na dare.
Gwamnatin Jihar Kano ta ce babu wata kwakkwarar hujja da aka samu daga takardun karar ‘yan sanda da ke tuhumar shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa da laifin kisan kai kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane a mazabar sa a zaben 2023. Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Musa Abdullahi Lawan, shine ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau, inda ya kara da cewa an samu kura-kurai sosai bayanan shaidun gani da ido. Lawal ya ce gwamnatin jihar na da isassun hujjoji da ke nuna cewa magoya bayan NNPP ciki har da wadanda
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta kammala bincike na farko kan Fatima Malam, wadda ake zargin ta dabawa Sharifah Usman ‘yar shekara 8 wuka.
Muddin ba wani sauya aka samu na gaggawa ba, Ministan sufurin jiragen sama ya ce jirgin saman Najeriya Air zai iso kasarnan a gobe Juma'a.
Karamin ministan kwadago mai barin gado, Festus Keyamo, yace nadin karamin minister da shugaban kasa keyi baya kan doron kundin tsarin mulki.
Zababben shugaban kasa, Tinubu da mataimakinsa zababben shugaban kasa, Kashim Shetima sun karbi lambar girmamawa ta GCFR da GCON.
Gwamnatin Tarayya ta ce a yanzu ‘yan Najeriya zasu iya neman bankunan kasuwancinsu su buga musu katin cirar kudi na ATM wanda zai iya aiki matsayin katin shaidar zama dan kasa.
Jami’an hukumar tsaro dake bada kariya ga fararen hula Civil Defence reshen jihar Kano sunyi nasarar kama wasu mutane biyar da ake zargin barayin waya ne.
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta dage jigilar kaso na farko na maniyyata daga yau zuwa 3 ga watan gobe na Yuni.
Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta umarci dukkanin manyan makarantun kasarnan da su bada guraben karatu ga daliban Najeriya da suka tsere daga yakin Sudan.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.
Kwanaki biyar gabanin karewar wa'adin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministoci sun fara mika ragamar aiki ga manyan sakatarori a ma'aikatunsu gabanin rushe majalisar zartaswa.
Kungiyar matasa mai zaman kanta ta dake rajin yaki da cututtuka masu yaduwa da matsalolin al’umma YOSPIS, na kira ga zababben gwamnan jihar Kano mai jiran gadon Engr. Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar ta-baci a kan Annobar kwacen waya ta hanyar kafa wani kwamitin kwarta kwana da zai yi aiki tare da ‘yan sanda da bangaren shari’a domin gudanar da bincike cikin gaggawa, tare da gurfanar da masu laifi a gaban shari’a.
Gwamnatin Tarayya na iya yin Tsumin kusan Naira Trilliyan 7 a duk shekara da kuma Naira trilliyan 35 na jimillhar kashe kudade a kasafin kudi nan da shekaru biyar masu zuwa sakamakon fara aiki da matatar Dangote.
Jam’iyyar PDP ta ce kin amincewa da bukatar da ta yi na nuna yadda ake shari’ar karrakin zaben shugaban kasa kai tsaye ba wani koma-baya ba ne.
Gwamnatin jihar Edo ta kori malamai 13 na jami’ar Ambrose Ali daga bakin aiki, bisa laifukan da suka hada da karyar shekaru da zamba da rashin ‘Da’a da cin zarafi da kuma musgunawa dalibai.
“Kuna da sauran wa’adi daga yanzu zuwa ranar Juma'a, 26 ga watan Mayu da muke ciki na 2023, ku mika al'amuran hukumomin ku ga manyan sakatarori ko Daraktocin mulki da kudi.
Hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa UBEC ta ce samun hakikanin adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ba zai yiwu ba sai an yi kidayar jama’a.
Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado ba zai amince da sabon kudirin karawa ma’ikata shekarun Ritaya zuwa shekaru 65 ba.
Garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin shiri yayin da mazauna garin ke jiran tarbar dansu wanda wa'adinsa na shekaru takwas zai kare a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabuwar matatar mai ta Dangote a yau Litinin, wadda ake sa ran zata tace gangar mai dubu 650 kowacce rana domin rage wahalar shigo da tacaccen mai cikin kasarnan.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta ce sama da kashi 70 cikin 100 na kayan abincin da ake fitarwa daga Najeriya ana ki amincewa da su a kasashen waje.
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa NARD ta dakatar da yajin aikin gargadi da take gudanarwa na kwanaki biyar.
Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya samar da ma’aikatar harkokin addinai a matsayin hanyar samar da matakan magance rashin jituwa tsakanin addinai a fadin kasar nan.
Kungiyar Malaman Makarantun Fasaha ta ASUP, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rattaba hannu a kan dokar da za ta soke bambancin dake tsakanin shaidar digiri ta BSC da HND kafin ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Tawagar farko ta jami’ai 31 na Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, sun tashi zuwa kasar Saudiyya daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, gabanin fara jigilar maniyatan 2023.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bada takardar daukar aiki kai tsaye ga wasu masu aikin hidimtawa kasa guda 65.
A ranar Alhamis mai zuwa ce, Za’a karrama zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da lambar girmamawa ta kasa GCFR, da kuma mataimakinsa Kashim Shettima wanda za’a bashi lambar girmamawa ta GCON.
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB, ta ce daga yanzu ya zama wajibi masu neman shiga jami’a kai tsaye su rika rubuta jarabawar UTME , tare da sauran wadanda suke zama domin rubuta jarabawar.
Hukumar Kidaya ta kasa ta ce ta kashe jimillar kudi har naira milyan dubu 200 domin kimtsawa aikin kidayar mutane da gidaje ta shekarar bana, kamar yadda shugaban hukumar Nasir Kwarra ya baiyyana.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC , ta ce a yanzu haka tana kan binciken gwamnan jihar Zamfara, mai shirin barin gado, Bello Matawalle saboda zarginsa da yin awon gaba da tsabar kudi, naira da gugar naira har milyan dubu 70.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, Ya soke shaidar takardar mallakar fili ta wasu kanfanoni guda tara, mallakin tsohon gwamnan jihar Sanata Ahmed Muhammed Makarfi.
Shugabancin jam’iyyar Labour na kasa tsagin Lamidi Apapa, Ya musanta karbar naira milyan 500 daga hannun wani mutum, domin wargaza karar da jam’iyyar ta shigar a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa.
Tsohon ministan lafiya a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, Chief Gabriel Aduku ya zama sabon shugaban kungiyar tuntuba ta Arewacin kasar nan.
Gwamnatin taraiyya ta yi barazanar daukar Hayar Likitoci tare da biyansu albashi da hakkokin Likitoci masu neman kwarewa da suka shiga yajin aiki.
Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai na ranar Talata a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato ya karu zuwa 85, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace a yankunan da lamarin ya shafa.
Majalisar zartarwa na kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da jinginar da filayen sauka da tashin jiragen sama Nnamdi Azikwe dake Abuja da kuma filin jirgin sama Mallam Aminu Kano dake nan nan Kano.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar wakilai Alhasan Ado doguwa ya janye daga takarar kujerar kakakin majalisar wakilai ta kasa.
A ranar 9 ga watan Yuni na shekarar 2020 mai Shari'a Honorable Justice Allagoa ya zartas da cewa ba a...
Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta ce jami’an tsaro...
Hukumomi sun ce an tura ƙarin jami'an tsaro a yankin
Ya ce yana neman tsayawa takarar domin inganta rayuwar 'yan Najeriya...
Cikin Fasinjojin akwai wani mutum da ake kyautata zatton dan Asia ne da kuma
Idan za’a iya tunawa dai a watan Ramadan na bara ne...
Yace sun kama jarkokin burkutu da aka haɗa a matsayin giya.
Ta cikin wani Video na kasa da minti 2 da suka fitar da Maraicen ranar laraba
Muna Adduar Allah ya takaita dakuma samun lafiya ga dukkanin wadanda suke dauke da ita dama sauran cututtuka.
Ana Sauraren Jawaban Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kai tsaye. Wanda yake jawabai kan Annobar Cutar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a dazu kenan yayin zantawa da ministan Lafiya da kuma shugaban Hukumar yaki da cututtuka ta NCDC a fadar mulkin kasa ta Villa.
Wasu na kiran cewa ya kamata a kawo karin dakunan binciken zuwa Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Gabas.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, yayin da ya halarci taron kaddamar kwamitin dake da alhakin tattara kudade na gudun mowar yakar cutar Coronavirus.
Gwamna Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya fita duba yadda aikin rufe iyakokin Kano yake gudana
Abuja, inda ya nuna Fasahar da ta zama cikin wadanda sukayi fice a gasar
An kuma garzaya da wasu 'yan sanda biyu da suka ji raunuka a hadarin zuwa Asibiti
© Copyright 2023 Steam Broadcasting and Communications Limited. Powered by Aiir.