On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Abduljabbar Kabara Ya Sake Korar Lauyoyinsa

Abduljabbar Nasiru Kabara

Wata Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Kano ta umarci hukumar bada tallafin shari’a kyauta ta samar da Lauya da zai cigaba da kare sheik Abduljabbar Nasiru Kabara, a cigaba da shari’ar da ake yi kan zargin sa da yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Gwamnatin jihar Kano tana tuhumar Kabara da aikata laifuka guda hudu da suka hada da furta kalaman batanci ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhd (S.A.W) a ranar 10 ga watan Augusta da 25 ga watan October da kuma 20 ga watan Disamba shekarar 2019.

A yayin da ake cigaba da zaman, wanda ake karar ya bayyanawa kotun cewa lauyan ya daina wakiltar sa ne sakamakon wasu koke-koke da ya ya rubuta a kansa.

Kabara ya zargi Lauyoyinsa da sabawa dokar aiki tare da tatsar kudi daga hannun sa.