On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 100 Da Gonaki Masu Yawa A Jihar Bauchi

HOTON AMBALIYA

Kimanin gidaje 100 da kuma tarin Gonaki ne ambaliyar ruwa ta lalata a karamar hukumar Darazo dake jihar Bauchi.

Mukaddashin Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa  ta jihar Bauchi, Alhaji Bala Lame ya fadawa manema Labarai cewa, an samu ambaliyar ruwan ne  biyo bayan  mamakon ruwa sama kamar da bakin kwarya da aka rika samu a yankin har tsawon kwanaki 3.

Yace tuni jami’an hukumar suka ziyarci yankin da abun ya shafa sannan kuma sun kididdige irin asarar da ambaliyar ruwan  ta haddasa, yayin daga bisani zasu rubuta rahoton domin yuyuwar samun tallafin gwamnati.

Sai dai kuma yace ba’a samu rahoton asarar  rai ko jikkata  ko kuma bacewar mutane ba, inda daga karshe yaja  hankalin jama’a da su guji yin gini akan hanyoyin ruwa da kuma zuba shara a cikin magudan ruwa.

More from Labarai