On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Bada Hutun Makarantu Da Ma'aikata A Jahohin Borno Da Legas Domin Karbar Katin Zabe - Najeriya 2023

Ma’aikatar ilimi ta jihar Borno ta bayar da hutun kwanaki takwas ga makarantu a fadin jihar gabanin babban zabe na 2023 mai gabatowa, yayinda a legas akabada hutu ga ma'aikatan gwamnati

A cikin wata wasika mai dauke da sahannun Daraktan kula da makarantu na ma’aikatar ilimi ta jihar Borno, Mustapha Umara, ya bayyana cewa hutun zai baiwa ma’aikata da daliban da suka cancanta damar tabbatar da ‘yancinsu na ‘yan kasa.

Wasikar tace an dauki matakin ne domin baiwa ma’aikata da daliban da suka cancanta damar yin amfani da ‘yancinsu  da kuma bada damar amfani da makarantu a matsayin cibiyoyin karbar katinan zabe.

Itama gwamnatin jihar Legas ta ayyana  kwanaki hudu amatsayin hutu ga ma’aikatan gwamnati domin basu damar karbar katin zabe na dindindin a kananan hukumominsu.

Shugaban ma’aikatan, Hakeem Muri-Okunola, wanda ya tabbatar da hakan a wata takardar da aka fitar a ranar Laraba, ya ce gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya nuna farin cikinsa tare da amincewa  da ranakun hutu ga  ma’aikatan gwamnati.

Ya yi bayanin cewa ranar da babu aiki za ta fara ne a ranar Talata 24 ga watan Janairu, kuma za ta kare ranar Juma’a 27 ga watan Janairu ga ma’aikatan aji daban-daban na gwamnati.

Muri-Okunola ya ce ya umarci hukumomi da su ba wa jami’ansu damar zuwa karbar katin zabe.