On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Bawa Ma'aikata Hutun Kwana Biyu A Jihar Borno

GWAMNA ZULUM NA JIHAR BORNO

Gwamnatin jihar Borno ta Aiyana Ranakun Alhamis da Juma’a mai zuwa a matsayin ranakun Hutu ga ma’aikatan jihar domin samun sukunin yin rijistar katin zabensu na din-din ga wadanda basu dashi .

Bayar da hutun na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun shugaban Ma’aikatan jihar, Mister Simon Malgwi.

Sanarwar ta bukaci Ma’aikatan gwamnati da sauran masu rike da madafun iko dasu yi amfani da damar wajen tabbatar da cewa sun mallaki katin zabensu na din-din, wanda zai basu damar zabar yancinsu a matsayin sun a yan kasa.

Kazalika an bukaci daukacin jama'ar jihar da suka san basu da katin zaben ko kuma zasu yi gyara dasu gaggauta yin hakan kafin karewar  wa'adin da hukumar zabe ta kas mai zaman kanta ta bayar.

More from Labarai