On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Bawa Wani 'Kasurgumin Dan Ta’adda Sarauta A jihar Zamfara

MAI GARKUWA DA MUTANE

Masarautar Yan Doton Daji dake jihar Zamfara ta nada wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, mai suna Ado Aleiro a matsayin sarkin Fulanin Yandoto

Daukar matakin dora shi kan sarautar ya biyo bayan, irin rawar da  ya taka  a yayin wani gangamin samar da zaman lafiya  da aka shirya tsakanin masarautar da kuma  ‘yan ta’addar da suka addabi karamar hukumar Tsafe.

Wata majiya daga masarautar  ta fadawa jaridar Daily trust cewa, Gwamnatin jihar ta bada umarnin dakatar da nadin sarautar akan Aleiro, bisa fargabar samun tunzurin mutane, bayan da bayanan bada sarautar suka fita kafafen yada labarai.

A lokacin da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Danmusa, Sanusi Dingi, ya tabbatar da cewa, Yan ta’addar ne suka  shirya  yarjejeniyar zaman lafiyar da kansu ta karkashin  shugabannin Fulani dake yankin.

More from Labarai