On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Binne Gawar Matashin nan Dake Shara a Asibitin Sojin Sama dake Kano, Wanda Ya Mutu Bayan Duka Da Ake Zargin Ya Sha a Hannun Wani Soja

Marigayi Yusuf Shu'aibu

Watakila akwai sauran bayanai da ba’a sani ba game da rasuwar Shu’aibu Yusuf, wani ma’aikacin farar hula a Asibitin Sojojin sama da ke Kano bayan duka da ake zargin wani sojan sama da yi ma sa.

Arewa Radio ta gano cewa sai a ranar Larabar da ta gabata akayi  jana'izar marigayi Yusuf, mako guda bayan rasuwarsa, bayan da aka gudanar da bincike kan  gawar don gano musabbabin mutuwarsa.

A rahotonmu na musamman na wannan mako, wakilinmu  Abdulraman Balarabe Isah ya ji ta bakin ‘yan uwan marigayi Yusuf kuma sun dage cewa, zasu bibiyi hakkin matashin domin tabbatar da cewa doka ta yi aiki akan wanda ake zargi idan har aka kama shi laifi.

Abu guda da zai hakukurtar da ‘yan uwan marigayi Yusuf shine ganin an hukunta jami’in sojan saman kasar nan da aka bayyana da suna Aminu, wanda ake zargi da lakadawa dan nasu duka, wanda daga bisani Allah ya karbi ran sa.

Hakan ce ta sa suka jinkirta yiwa gawar sutura tare da kashe kusan naira dubu 200 domin gudanar da bincike da nufin gano musabbabin mutuwar ta sa.

Matar mahaifin sa, wacce ta rike shi bayan rasuwar mahaifiyar sa ta labartawa Arewa Radio yadda abin ya kasance, kamar yadda taji daga bakin dan nata. Insert…

A cewar ta, Yusuf mai shekaru 23 na haihuwa a duniya, ya za’ku ya koma gida daga asibitin sojojin saman na nan Kano, inda yake aiki a matsayin mai shara bayan ya kammala aikin dare da yayi, sai dai Oga Aminu ya bukaci ya kara yi masa wani aiki duk da cewa lokacin aikin sa ya wuce.

A sakamakon haka ne yar jayayya ta barke a tsakanin marigayi Yusuf, wanda yake farar hula da kuma sojan dake da horo na musamman, wanda rahotanni suka ce ya sawa marigayin hannu har ya zubar masa da jini.

“Na ga rigar sa duk jini kuma bakin sa a kumbure kuma da na tambaye yace mun soja ne ya masa haka saboda ya nemi ya tilasta masa yin aiki bayan lokacin aikin sa ya wuce.”

“Muna tare da shi har dare, sannan ya shiga dakin sa ya kwanta, shikenan bai tashi ba, sai gawar sa muka gani.”

Shima wani aminin Yusuf mai suna Usman Mohammad, wanda ya fara haduwa da shi a hanyar sa ta shiga gida daga wajen aiki ya tabbatar da cewa rigar marigayin ta kasance cikin jinni bayan kumburi da ya cika fuskar sa.

“Dama bisa al’ada ya kan tsaya a waje na kafin ya shiga gida a ko da yaushe. To a ranar sai na lura cewa gaba daya jini ne a rigar sa da kuma kumburi sosai a bakin sa, shine yake ce mun ai wani soja ne masa haka. Ya ce bayan y agama aikin dare, yana shirin tafiya gida da safe, sojan yace da shi ya tsaya yayi masa wani aiki kuma duk da ya fadawa sojan cewa lokacin aikin sa ya wuce, sai da ya tsaya yayi aikin.”

“Ya gama aikin nan da ya sa shi, sai ya kara cewa ya tsaya yayi wani aikin, a nan ne yace, shifa gaskiya ba zai iya ba don yunwa yake ji, sai dai idan sojan zai ba shi abincin da zai ci. Juyawar sa, da nufin zai tafi ke da wuya, sojan ya hau kan sa da duka, kamar yadda ya fada mun.”

Mutuwar matashin ta haihar da wata zanga-zanga a unguwar, inda mazauna yankin suka rufe titin zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na malam Aminu Kano domin nuna rashin jin dadin su akan abinda ya faru.

Yayinda ‘yanuwan Yusuf suka damu wajen sanin hakikanin abinda ya kashe dan nasu, ita kuwa shalkwatar rundunar sojin saman ta kasa ta tabbatar da cewa tuni ta fara bincike domin bankado takamaiman abinda ya faru.

Yayinda binciken ke gudana, rundunar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa marin Yusuf kawai jami’in nata ya yi bayan da marigayin ya ki yin aikin da aka umarce shi ya yi.

Sai dai mahaifin Yusuf, Shu’aibu Bala Adamu, ya bayyana mamakin sa akan yadda mari zai illata mutum kamar yadda suka gani a jikin Yusuf bayan komawar sa gida kafin Al… ya karbi ran sa.

“Ka kaddara cewa marin Yusuf kawai aka yi kamar yadda suka fada, an dai mare shin ko? Kuma hakan ne sanadiyar mutuwar tasa koh? Ai kaga abu ya rataya akan wanda yayi abun nan saboda shine sila.”

Adamu, wanda ya ce suna sa ran samun sakamakon binciken gawar da aka gudanar nan da makonni biyu, yana mai cewa sai sun ga abunda ya turewa buzu nadi wajen tabbatar da cewa an hukunta wanda ake zargi da aikata wannan danyen aikin akan babban dan nasa.

Mazauna yankin dai na cigaba da kira ga mahukunta da abin ya shafa da su tabbatar da cewa an gudanar da bincike yadda ya kamata tare da hukunta wanda ake zargi idan aka kamashi da laifin, domin hakan ya zama izina ga saura.