On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Bukaci Kotu Ta Hana Sauya Sunan Kabiru Masari Daga Matsayin Mataimakin Tinubu.

HOTON APC DA KOTU

An bukaci Wata Babbar Kotun Taraiyya mai zamanta a Abuja, data hana jam’iyyar APC maye gurbin sunan Kabiru Masari da wani mutum na daban, a matsayin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Wasu kusoshin jam’iyyar  biyu, sannan kuma wakilanta a zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka yi a kwanakin baya, Zakari Maigari da Kuma Zubainatu Mohammed ne suka garzaya gaban kotun, domin ganin ta hana hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta karbar  canjin sunan  dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Bugu da kari sun bukaci kotu  data yi bayani akan ko ya halatta a dokance, Kabiru Masari ya janye daga takarar mataimakin shugaban kasa, domin bawa jam’iyyar APCn damar canza shi da wani mutum na daban.

Idan har wannan shari’a  tayi aiki, Ka iya shafar jam’iyyar  LP wadda itama ta aiyana Doyin Okupe a matsayin Dan takarar Mataimakin ta na shugaban kasa, ammafa  na wucin gadi.