On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Cire Najeriya Daga Cikin Kasashen Da Zasu Amfana Daga Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro Na Afirka

Gavi, ƙungiyar rigakafi da  UNICEF ta ce ta ware allurai miliyan 18 na rigakafin cutar maleriya ga ƙasashen Afirka 12 a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Sai dai Najeriya ba ta cikin wadanda za su amfana.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, Gavi ta ce yayin da akalla kasashen Afirka 28 suka nuna sha'awar karbar maganin zazzabin cizon sauron, an kayyade rabon ne ta hanyar ba da fifiko ga wuraren da ake bukata.

Kungiyar ta ce tun daga shekarar 2019, yara miliyan 1.7 a kasashen Ghana, Kenya da Malawi sun karbi maganin ta hanyar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro.

A cewar Gavi, rabon alluran rigakafin na miliyan 18 zai baiwa wasu kasashe tara damar shigar da allurar a cikin shirye-shiryensu na rigakafi na yau da kullun a karon farko.

Kasashe 9 sun hada da Benin, Burkina Faso, Burundi, Kamaru, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Laberiya, Nijar, Saliyo da Uganda.