On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Dage Lokacin Ganawa Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Kungiyoyin Kwadago

An dage ganawar da aka shirya yi tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya, dangane da alkawarin da bangarorin biyu suka kulla na biyawa kungiyoyin kwadago bukatunsu kafin cikar wa’adin kwanaki 30.

Wani babban jami’in kungiyar kwadago, wanda ya zanta da jaridar PUNCH, ya ce a  halin yanzu za’a yi ganawar  nea  Talatar makon gobe.

Jami’in wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce an dage ganawar  ne kasancewar, ranar  litinin da aka tsara yin taron ita  ce lokacin da ake  gudanar da zaman majalisar zartawa  na kasa.

Ya sake  jaddada matsayarsu na daukar matakin da  ya dace  da zarar wa’adin da suka bayar  yak are muddin ba  biya masu bukatunsu ba.