On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Dage Lokacin Rubuta Jarabawar Qualifying A Kano

An dage lokacin rubuta jarabawar Qualifying ta manyan makarantun sakandire a jihar Kano, wadda aka tsara gudanarwa a jiya, har sai abunda hali ya yi.

Ma’aikatar  Ilimi ta jihar kano ce ta sanar  dage  rubuta  jarabawar bisa  dalilai  na yajin aikin da gamaiyyar kungiyoyin kwadago na  NLC da TUC suka shiga a fadin kasa.

Sanarwar da kakakin Ma’aikatar  Balarabe Abdullahi Kiru  ya fitar, Ta roki  Dalibai da iyaye  da  su yi hakuri  da yanayin da aka  tsinci  kai a saboda dage lokacin rubuta jarabawar.