On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Dakatar Da Sarkin Da Ya Bawa Wani 'Dan Ta'adda Sarauta A Jihar Zamfara

ALERO

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara, Ya amince da Dakatar da Sarkin sabuwar Masarautar Birnin Yandoto, Alhaji Aliyu Marafa, bisa ga sarautar da ya bawa wani jagoran ‘yan ta’adda a yankin da ake nema ruwa a jallo, mai suna Adamu Aliero Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero.

Idan ba’a manta ba, a shekarar  2020 ne gwamnatin jihar Zamfara ta aiyana Alero a matsayin wanda take nema ruwa a jallo sakamakon yawaitar  kashe-kashe  da kuma  garkuwa da mutane da ake samu  a yankunan dake zamfara da kuma jihar Katsina.

A ranar Asabar din data gabata ce, aka nada Alero a matsayin sarkin Fulanin Yandoto,Sai dai kuma yan sa’oi kadan da yin nadin, masarautar ta bada sanarwar  dakatar  da sarautar. Rahotanni na baiyana  shugabanni  ‘yan ta’adda  daban daban ne suka halarci  bikin bayar da sarautar da aka yi a lokacin.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar, Ta umarci Hakimin Yandoto Alhaji Mahe Garba Marafa  daya rike  harkokin tafiyar da masarautar kafin daukar mataki na gaba.

More from Labarai