On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Dawo Da Hasken Lantarki Bayan Daukewarsa Da Aka Samu A Fadin Kasa

LANTARKI

Kanfanin Samar da wutar Lantarki na kasa TCN ya baiyana cewa an samu nasarar dawo da wutar lantarki wadda ta dauke a ranar Litinin, sakamakon saukar kuzarin wutar lantarkin da aka samu

Ta cikin wata sanarwa da kanfanin ya fitar a daren  jiya,  Ya baiyana cewa wutar lantarkin ta dawo Tashoshin rarraba wutar lantarkin dake  Kaduna da Kano sai Osogbo da ta Ihovbor da Tashar  Jebba  sai ta Kainji  da Benin  da  Onisha da kuma ta Shiroro .

Sanarwar  ta  alakanta saukar kuzarin lantarkin da aka samu  da tangardar da aka samu a  wani layin  wuta da aka samu babu ba zato ba tsammani wanda  hakan ya haifar da matsalar.

A jiya ne kanfanonin rarraba hasken wutar lantarki suka bada sanar da abokan huldar su daukewar wutar lantarkin, a sakamakon saukar  kuzarin  lantarkin da aka samu a fadin kasa.

More from Labarai