On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Dena Jin 'Duriyar Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Sace Tun Bayan Kama Tukur Mamu

jirgin kasa

Rahotanni na baiyana cewa tun bayan kamawa da kuma tsare mai sasantawa da ‘Yan Bindiga, Tukur Mamu a makon jiya, Iyalai da dangin sauran fasinjojin jirgin kasar da yan bindiga suka sace a Kaduna, suka dena jin duriyar ‘yan uwan nasu.

Har yanzu ragowar Fasinjojin jirgin Kasa  23 da Yan Ta’adda  suka sace  na  tsare a hannunsu , a yayin da suke cika kwanaki 186 a wajensu.

Sama da fasinjojin jirgin kasa  60 ne aka sace a lokacin da Yan ta’addar suka kaima jirgin kasar hari lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa  Kaduna daga Abuja.

Rahotanni na baiyana cewa  mafi yawa daga cikin fasinjojin jirgin kasar da aka sako, kowannensu ya biya naira milyan 100, bayan shiga tsakanin da mai sasantawa da yan bindiga Tukur Mamu yayi.

TUKUR MAMU

TUKUR MAMU

Mohammed  Sabiu Barau  wanda ya kasance  kanin  wani mai aikin hidimtawa kasa ne da  har yanzu yake tsare a hannun yan bindigar, yace a yayin da dangin dan uwan nasu ke  fatan sake  saduwa  dashi  a lokacin da aka sako shi, a halin yanzu babu abunda suke kan yi illa barin komi  ga  ubangiji domin kawo masu dauki.