On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Gabatar Da Sabbin Takardun Kudi Na Naira A Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da sabbin takardun kudi na Naira dubu daya (1000) da Naira dari biyar (500) da kuma Naira dari biyu (200).

An gabatar da sabbin kudin a fadar shugaban kasar ta Aso Villa dake birnin Abuja da safiyar ranar Laraba.

Gwamnan Babban Bankin kasa CBN  Godwin Emefiele, yace bankin ba zai sauya wa’adinsa ba na mayar da duk tsofaffin takardun kudi zuwa bankunan kasuwanci domin musayarsu da  sabbin takardun na Naira.

Za’a fara amfani da sabbin kudin a ranar 15 ga watan Disamba na shekarar 2022 yayinda za’a daina amfani da tsaffin daga ranar 31 ga watan Janairu na shekarar 2023.

Da yake jawabi yayin bikin gabatar da samfurin kudin da aka sake fasaltawa, gwamnan bankin CBN, yace sake fasalin Naira nada alfanu.

Cikin amfani sake fasalin acewar Emefele akwai magance buga jabun kudi da rage hauhawar farashi sannan za’a rika biya da sanya ido kan yadda kudi ke zagayawa a hannun jama’a.