On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Gano Gawarwaki 9 Bayan Hatsarin Kwale-Kwale A Shiroro - NSEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta ce an gano gawarwaki 9 a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Shiroro da ke jihar.

Shugaban hukumar NSEMA, Alhaji Salihu Garba ne ya bayyana hakan a wata zantawa da kamfanin dillancin labaru na kasa NAN a  Minna ranar Lahadi.

Idan za’a iya tunawa, Rahoton NAN yace an  tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda al’amarin ya rutsa da su, ‘yan kasuwa ne, suna jigilar kaya ne daga unguwar Zongoru da ke gundumar Bassa zuwa Gijiwa, gabanin kasuwar Juma’a da ke Kuta, shalkwatar karamar hukumar Shiroro, a lokacin da al’amarin ya faru.