On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Kaddamar Da Sabuwar Kungiyar Kwallon Kafa A Kano Kumbotso Stars.

Karamar hukumar Kumbotso ta kaddamar da sabuwar kungiyar kwallon kafa ta 'yan wasan yankin lakabin Kumbotso Stars da ake saran zai yi fice tare da samun nasara a matakin Jihar Kano da Kasa da ma duniya baki daya.

Da yake kaddamar da sabuwar kungiyar ranar Juma'a,  shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Dr Kabiru Usaini Zawachiki ya ce sun samar da Kungiyar ta Kumbotso Stars ne domin samawa Matasa aikin yi tare da Samar da zaman lafiya a Karamar Hukumar ta Kumbotso.

Dr Usaini ya kara da cewa sun bawa Kungiyar sunan Kumbotso Stars ne domin a cigaba da Gudanar da Kungiyar ko bayan basa nan, tare  da ba su duk abubuwan da ake bukata wajan gudanar da harkokin wasan Kwallon Kafa,

Bugu da Kari Dr Usaini ya ce sun ware musu aluwus aluwus a lokacin bada horo, sun kuma dauko 'yan wasan daga kowanne bangare na Karamar Hukumar Kumbotso bayan tantancewa.

Da yake zantawa da wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya, mai baiwa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin Matasa da wassanni Yusuf Imam Ogan boye ya ce Gwamnatin Jahar Kano za ta tallafawa Kungiyar ta Kumbotso Stars, tare da ƙoƙarin  samar da irin wadannan Kungiyoyin Kwallon Kafa a daukacin kananan hukumomin Jahar.