On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Kai Hari Gidan Gyaran Hali Na Kuje Dake Abuja

Gidan Gyaran Hali Na Kuje

Nan kuma an jiyo karar fashewar wasu abubuwa da kuma harbin bindiga a kusa da Gidan Gyaran Hali na Kuje dake Abuja babban birnin taraiyya a daren jiya.

Duk da cewar har yanzu akwai ‘kanfar cikakken bayanin abunda ya faru, sai dai mazauna yankin sun fadawa manema Labarai cewa,  harbin bindigar ya shafe  tsawon mintina  20.

Mazauna yankin sunyi fargabar cewa, Yan Bindiga ne suka kaiwa gidan gyaran halin farmaki.

A yanzu haka  Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa ta tabbatar da harin da aka kai, kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa  da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Abubakar Umar ya fitar.

Sanarwar tace wasu ‘yan ta’adda da ba’a san ko su waye ba sun kaiwa  gidan gyaran hali na kuje  hari da karfe  10 na dare, sai dai kuma jami’an tsaro  sun samu nasarar  dakile  harin.

Kazalika yace a yanzu haka an samu dawowar zaman lafiya, inda yayi alkawarin fitar da cikakkun bayanai akan harin nan bada jimawa ba.

 

 

More from Labarai