On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Kaiwa Ayarin Motocin Jami’an Shugaban Kasa Hari.

Hoton masu tsaron lafiyar Shugaban Kasa

‘Yan Ta’adda sun yiwa Ayarin motocin jami’an dake tarbar shugaban kasa harin kwantan ‘bauna, tawagar jami’an sun hada da jami’an tsaro da ‘yan Jarida da kuma masu tsara harkokin tarbar baki na fadar shugaban kasa.

Harin kwantan baunar da ‘Yan Ta’adda suka kaddamar a  kusa da garin Dutsinma dake jihar Katsina  yayi sanadin mutuwar  jami’an yansanda biyu. Fadar  shugaban Kasa ta baiyana cewa  tawagar  ayarin jami’an dake  tarbar shugaban kasar  na kan hanyarsu ne  ta zuwa  Daura Mahaifar shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda zai je can domin yin Idin Babbar Sallah, amma shugaban kasar baya cikin ayarin.

Babban Mataimaki na Musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada Labarai da kuma wayar da kai, Malam Garba Shehu  ya tabbatar da kai harin ta cikin wata sanarwa  da  ya  fitar, Yace  Maharan  sun yiwa  ayarin jami’an  dake tarbar shugaban kasar kwantan bauna, tare da bude masu wuta babu kakkautawa, sai dai kuma sojoji da jami’an yansanda da kuma jami’an tsaron farin kaya na DSS  dake cikin tawagar  sun dakile harin.

Garba Shehu ya baiyana cewa  mutane biyu ne kadai suka samu ‘yan raunika, To sai dai Kakakin Rundunar Yansandan Jihar Katsina, Gambo Isah a wata sanarwa  da ya fitar, Yace Baturen Yansandan yankin tare da wani mutum daya na daga cikin wadanda aka halaka a yayin harin kwantan baunan.

 

More from Labarai