On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

An Kama Wani Mutum Yana Wanka Da Jini

Rundunar yansandan jihar Ogun ta cafke wani mutum dan shekara 49 a duniya mai suna Ganiyu Shina saboda yin wanka da jini a wani kogi dake yankin Kotopo na karamar hukumar Odeda.

An dakume mutumin ne, bayan da mutanen yankin suka ganshi ya ajiye motarsa a gefen kogin, Sannan ya fito da wata jarka cike da jini, inda ya fara yin wanka da shi.

Sanarwar da jami’an yansanda suka fitar ta baiyana cewa, wanda ake tuhumar yayi ikirarin cewar yana tabin Aljanu, Sannan kuma wani Boka  ya bashi umarnin yin wanka da jinin Saniya bana mutum ba.

Kwamishinan yansandna jihar Lanre Bankole ya bada umarnin daukar ragowar jinin domin yin gwaji akansa, domin tabbatar da jinin na mutum ne ko kuma saniya.