On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An 'Kara Tura Jami'an 'Yansanda Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

POLICE

Babban Sufeton ‘Yansanda na kasa, Usman Alkali Baba, Ya kar tura tawagar Jami’an Yansanda domin inganta sha’anin tsaro akan babbar Hanyar Abuja zuwa Kaduna, domin dakile matsalolin da suka shafi aikata lefukan Garkuwa da mutane da kuma fashin Daji.

Da yake  yiwa jami’an Yansandan da aka tura jawabi yau  a shalkwatar Rundunar Yansanda ta kasa dake Abuja, Kwamishinan rundunar mai kula da harkokin tura  jami’an Yansanda aiki, CP Mathew Akinyoshola, Ya bukace su dasu kasance a cikin shiri a kowane lokaci domin   cigaba da sauke nauyin da aka dora masu.

Kazalika yaja hankalin jami’an yansandan dasu kasance masu kyakykyawar mu’amma tare da nuna kwazo a wajen gudanar da aikinsu, tare da sanya kafar wando daya da duk wasu mutane dake kawo  barazana  ga cigaban zaman Lafiya da kuma tsaron kasa.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna, ta jima tana fama da matsalolin hare-haren Yan Ta’adda  wadanda ke kashe mutanen da basu ba basu gani ba.

 

More from Labarai