On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Kone 'Daliba da Ran ta Sakamakon Batanci ga Annabi a Sokoto

Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari Dake Jihar Sokoto

An kone wata ‘Daliba da ranta a kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake jihar Sokoto sakamakon zargin yin batanci ga Annabi.

Rahotanni sunce dalibar mai suna Deborah tayi batanci ga Annabi ta cikin wani zauren dandalin sada zumunta na Whatsapp da abokan karatunta suka kirkira domin tattauna batutuwan da suka shafi makarantar da karatunsu.

Wani a cikin zauren ya yi tsokaci kan abunda ya shafi Addini inda Deborah ta kalubalanci kalaman, harma tayi batanci akan Fiyayyen Halitti Annabi Muhammad (S.A.W)

Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar kwamishinan ilimi na jihar Sokoto Isah Bajini Galadanci, yace gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya bada umarnin a rufe makarantar ba tare da bata lokaci ba sannan jami’an hukumomin tsaro su gudanar da bincike.