On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Kori 'Yan Sanda 7 Daga Bakin Aiki A Najeriya

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda PSC, ta kori wasu manyan jami’an ‘yan sanda bakwai sakamakon samun su da aikata rashin da’a.

An yanke shawarar ne a yayin babban taron hukumar karo na 15.

Taron wanda shugabar riko, mai shari’a Clara Ogunbiyi ta jagoranta, ya yi la’akari da duk wasu batutuwan da suka shafi ladabtarwa da ke gaban hukumar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron a Abuja, kakakin hukumar, Ikechukwu Ani ya ce jami’an da aka kora sun hada da: CSP guda daya,  SP guda daya, da  ASP guda biyar.

Ya kara da cewa SP daya shima ya yi ritaya. Hukumar ta kuma rage masu mukamin CSP guda daya zuwa SP, sai SP guda uku zuwa DSP, sai kuma DSP guda biyu zuwa ASP.

Hukumar ta kuma rage wa masu mukamin ASP guda hudu zuwa sufeto.

An yanke wa manyan jami’an ‘yan sanda 10 da suka hada da ACP, CSP, SP da DSP guda biyu hukuncin mai tsauri, ciki har da masu mukamin ASP.

Mai shari’a Ogunbiyi ta yi kira ga jami’an ‘yan sanda da su tabbatar da cewa suna aiki bisa ka’idojin da aka kafa tare da kaucewa daukar doka a hannunsu.

Ta ce hukumar za ta ci gaba da yin aiki don dorewar kwararrun ‘yan sandan da ke aiki daidai da ka’idoji da da aka kafa tare da bin kyawawan ayyuka na kasa da kasa.