On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Kubutar Da Mata 10 Tare Da Wani Karamin Yaro Daga Hannun 'Yan Bindiga A Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce tayi nasarar kubutar da mata 10 da wani yaro dan shekara daya daga hannun masu garkuwa da mutane.

Wannan ceton ya biyo bayan nasarar da aka samu a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar. 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Asabar 

Shehu ya ce gungun ‘yan ta’adda sun kai farmaki kauyen Manye da ke karamar hukumar Anka a ranar Litinin 17 ga watan Oktoba,  inda suka yi garkuwa da mata goma da yaro dan shekara daya zuwa dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum na jihar inda suka kwashe kwanaki uku a hannunsu.