On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Kwaso 'Yan Najeriya 178 Daga Kasar Libiya

NEMA

Hukumar Bayar Da Agajin gaggawa ta Kasa, NEMA,Ta karbi Yan Najeriya 178 da suka makale a kasar Libiya a filin Tashi da Saukar Jiragen sama na Murtala Muhammad dake birnin Ikko.

Shugaban Hukumar, Alhaji Mustapha Ahmed ne ya tabbatar da haka a yayin hirirasa da manema Labarai a Legas.

Shugaban wanda ya samu wakilcin  jami’an Hukumar mai kula da jihar Legas, Ibrahim Farinloye, Yace  mutanen sun sauka filin jirgin ne a sashin sauke kayayyaki na filin da karfe 6 da mintina 20 na yammacin ranar Laraba.

Ya kara da cewa daga cikin mutane 63 maza ne a yayin da 73 suka kasance mata, Sai kuma Kanan Maza 15 da Yan Mata 13 sai jarirai mata 6 da Maza 8.

More from Labarai