On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

An Rufe Sansanonin 'Yan Gudun Hijira Hudu A Jihar Borno

SANSANIN YAN GUDUN HIJIRA

Gwamnatin jihar Borno ta ce ta rufe sansanonin ‘yan gudun hijira hudu tare da sake tsugunar da ‘Yan gudun Hijirar a wasu gidaje Dubu 11 data samar a wasu yankuna shida dake jihar.

Gwamna Babagana Zulum wanda ya yi jawabi a yayin rufe   sansanonin ‘yan gudun hijira hudu a ranar Alhamis a birnin  Maiduguri, ya ce an samu nasarar hakan ne biyo bayan dawowar zaman lafiya a jihar.

Gwamnan yace  sansanonin ‘yan gudun hijirar da aka rufe sun hada Dalori ta Daya sai Dalori  ta 2 da sansanin ‘yan gudun hijira dake kan hanyar zuwa  Gubio da Muna El-Badawi, inda ya ce a shekarar 2015  ne, mayakan Boko Haram suka raba mutanen da muhallansu.

Gwamnan ya danganta rufe sansanonin da matsalar  karancin kudade, inda ya kara da cewa a yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa  domin  rufe wasu sansanonin ‘yan gudun hijirar tare da mayar da mutanen garuruwansu na asali na da shekara ta 2023.