On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

An Sace Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Nasarawa

Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Nasarawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sace kwamishinan yada labarai da raya al’adu da kuma yawon bude ido na jihar Yakubu Lawal, da wasu ‘yan bindiga suka yi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar  ‘yan sandan jihar Nasarawa  DSP Ramhan Nansel  shine  ya tabbatar da haka ta  cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a safiyar yau a   Lafia babban birnin jihar.

Ya ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun yi awon gaba da kwamishinan yada labaran, bayan da  suka kai farmaki gidansa.

Ya kara da cewa a yanzu haka ana gudanar da bincike na hadin gwiwa tsakaninsu da jami’an tsaro baturen yansandan  Akwanga, ACP Halliru Aliyu domin ganin an kubutar da kwamishinan cikin salama sannan kuma a kama wadanda suka aikata lefin.