On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Samu Faduwar Farashin Kayayyaki A Najeriya - NBS

Hauhawar farashin kayyaki a Nigeria ta sauka zuwa kashi 21 a digo 34 cikin 100 a watan Disambar shekarra 2022, daga kashi 21 da digo 47 a watan Nuwamban shekarar, karo na farko cikin watanni 11.

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ce ta bayyana haka cikin rahoton hauhawar farashin da ta fitar, inda tace an samu saukar kashi 0 da digo 13, tsakanin watan Nuwamba da Disamba.

Idan za a tuna dai rahotan na watan Disambar 2022, ya bayyana yadda aka sa mu saukar farashin daga kashi 21 da digo 34 zuwa, idan aka kwatanta da kashi 21 da digo 47 da ake da shi a watan Disamba, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Kazalika a rahoton shekara shekara kuwa, hauhawar farashin ya kai kashi 5 sa digo 72, idan aka kwatanta dana watan Disambar 2021, wanda ya kai kashi 15 da digo 63, kuma ya tabbatar da karin tsadar kayayyakin a watan Disambar shekarar data gabata.