On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

An Ware Naira Milyan Dubu 30 A Matsayin Kudin Sallama Ga Yan Majalisar Dokoki Ta Kasa

YAN MAJALISA A Abuja

Wasu kungiyoyin farar hula sun yi All..h wadai da tsabar kudin da aka ware a cikin kunshin kasafin kudi har Naira biliyan 30 da milyan dari matsayin kudin sallama ga ‘yan majalisar dokoki ta kasa da kuma kaddamar da sabon zauren majalisa mai zuwa

A ranar Larabar da ta gabata ne majalisar dokoki  ta  kasa ta kara kudurin kasafin kudin shekarar 2023 daga Naira tiriliyan 20 da bilyan 51 zuwa Naira Tiriliyan 21 da bilyan  82, sannan ta amince da shi, wanda hakan ya nuna karin sama da Naira  Tiriliyan 1 da  bilyan  300  akan wanda  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a watan Oktoba.

Da yake tsokaci kan lamarin, Shugaban  kungiyar dake saka ido kan aiyukan  yan majalisa da kuma bada shawarwari  ta CISLAC, Auwal Rafsanjani, ya bayyana cewa abin takaici ne yadda majalisar kasa ta yi kasafin kudin da bai da wata alaka da jama’a,  Yana mai  cewa  tsarin anyi shine  kawai a salon nan na kashin dankali.