On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ana Amfani Da Maganin Kashe Kwari Mai Cutarwa A Najeriya Inji NAFDAC

Maganin Kashe Kwari

A bangaren kiwon lafiya kuwa, Hukumar kula da ingancin Abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta bukaci masu ruwa da tsaki dasu temaka mata wajen kawar da magungunan kashe kwari masu cutarwa a kasar nan.

Shugabar  hukumar,Uwar gida Mojisola  Adeyeye  ce  ta baiyana haka ta cikin wata sanarwa  mai dauke dasa  hannun kakakin hukumar  Olusayo Akintola  wadda aka fitar a ranar  lahadi,  Ta  baiyana damuwar ta  kan illolin dake  tattare  da  rashin yin amfani da magungunan kashe  kwarin  yadda  ya dace,wanda hakan ke shafar  samar da lafiyayyen kayan abinci a kasar  nan.

Mojisole Adeyeye  ta baiyana cewar, Binciken da wata  kungiya  mai suna Heinrich Boll Foundation ta  gabatar, Ya gano cewar kaso  40 bisa  100  na nau’ikan maganin kashe kwari da ake  amfani dasu a kasar  nan, an haramta  yin amfani dasu a kasashen turai.

Ta baiyana cewar  hukumar  NAFDAC  zata hada gwiwa da  masu bincike  da  masana domin  tattara bayanai da hujjoji kan matakan da ya kamata ta dauka akan irin  nau’ikan maganin kashe  kwarin masu cutarwa.