On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ana Kashe Kudi Sama Da Naira Tiriliyan 3 Duk Shekara Wajen Shigo Da Takardu Daga Kasashen Waje

Gwamnatin Tarayya tace hanya daya tilo da za ta ceto masana’antar samar da takardu da ta tabarbare ita ce a samu masu ruwa da tsaki su zuba jari a bangaren.

Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Niyi Adebayo shine ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani jawabi da ya gabatar a taron kasa da kasa  karo na farko a Abuja.

Adebayo, wanda daya daga cikin daraktoci a ma’aikatarsa, Francis Onuora ya wakilta a wurin taron, ya jaddada cewa gwamnati ta damu matuka cewa kashi 85 na kayayyakin da suka shafi takardu da ake amfani da su a cikin gida ana  shigo da su daga waje.

A cewarsa, ana kashe sama da Naira tiriliyan 3 a duk shekara wajen shigo da takardu daga kasashen waje, al’amarin da ba zai dore ba.

Ministan ya bayyana cewa a cikin manyan masana’antun samar da takardu  guda uku a Najeriya, daya c eke aiki  a matakin kashi 30 kacal.