On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Ana Musayar Yawu Tsakanin APC Da PDP Kan Makomar Takarar Bola Tinubu

Jam’iyyar APC tana zargin jam’iyyar adawa ta PDP da Labour Party da daukar nauyin labaran karya akan dan takararta na shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.

 

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na majalisar yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bayo Onanuga.

Hakan na zuwa ne bayan wata sanarwa ta bogi da aka yada ta yanar gizo a karshen mako wadda aka rawaito INEC tace tana binciken zargin da ake yi wa Tinubu, sai dai hukumar zaben  ta musanta.

Jam’iyyar APC ta ce za ta yaki duk wani labari na batanci ga dan takararta, yayin da ta kuma yi kira ga ‘yan sanda da su binciki bayanan na bogi da aka alakanta da INEC tare da gurfanar da duk wanda aka samu  laifi.

Sai dai Jam’iyya PDP ta maida martani akan zargen-zargen batanci da APC ke yi ma ta, tana mai cewa bata da hannu a dukannin Ikirarin, sai dai ta zargi APC da tsayar da  da dan takara da bai chanchanta ba a zaben 2023.

 Jam’iyyar PDP ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Rahotanni sun bayyana cewa an tuhumi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da laifin hada-hadar miyagun kwayoyi  a Amurka wanda wasu kungiyoyi ke neman a hana shi tsayawa takara saboda laifin.

Sai dai a makon da ya gabata, wata kotu a Amurka ta saki wasu kwafi na gaskiya na tuhume-tuhumen da ake yiwa Tinubu, amma  mai magana da yawun majalissar yakin neman zabensa Onanuga ya dage cewa an wanke shugaban nasa daga zargin.

Ita kuwa, hukumar zabe a kasar INEC ta yi watsi  da sanarwar da ta yi ikirarin cewa ta fara gudanar da bincike a kan wani laifi da ake zargin daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Hukumar a cikin wata sanarwa da kwamishinanta na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya fitar a Abuja, ya bayyana rahoton a matsayin na bogi wanda marasa kishi suka kitsa.

A cewarsa, sanarwar da aka fitar ba ta fito daga hukumar ba.

Okoye yace ana tura da sanarwar manema labarai daga hukumar ta INEC zuwa dandalin ‘yan jarida na INEC kuma a lokaci guda ana yada duk wata sanarwa  ta shafin hukumar da shafukan sada zumunta da aka tantance kuma aka amince.