On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ana Neman Hanyoyin Samarwa 'Yan Najeriya Sauki Daga Janye Tallafin Man Fetur

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta dakatar da shirin tafiya yajin aikin da ta tsara farawa daga gobe Laraba kan karin farashin man fetur sakamakon cire tallafin da ta yi.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin tarayya ta shigar da kara domin hana yajin aikin kuma kotu ta umarci NLC da kada ta shiga yajin aikin a ranar Litinin.

Dakatar da yajin aikin na daya daga cikin kudurori bakwai da aka cimma a ranar litinin bayan wata ganawa tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya.

Da yake karanta kudurin taron a daren jiya, shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya ce bangarorin biyu sun amince da kafa wani kwamitin hadin gwiwa da zai duba mafi karancin albashi.

Kwamitin zai kuma yi nazari kan shirin sauya fasalin iskar Gas da nazarin kalubalen samar da ilimi mai inganci da  aikin inganta ababen more rayuwa.

Shugaban kungiyar kwadago ta Kasa, NLC Jeo Ajero da TUC Festus Osifo sun amince da kudurin da aka cimma a ganawar da aka kammala tsakanin kungiyoyin da gwamnati.

Sai dai duk da haka ba su takamaimai ba game da buƙatun sake fasalin karin farashin man fetur.

Shugaban NLC ya yi kira a bada himma tare da maida hankalai don cimma wani madadi na man Fetur.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo ya bukaci gwamnati da ta kiyaye yarjejeniyar.

Baya ga aikin samar da tsarin kammala kula da matatun man kasarnan, bangarorin biyu sun amince da sake zama a ranar 19 ga wannan wata domin kara cimma matsaya kan aiwatar da tsarin.

Bayan dakatar da yajin aikin NLC, babu tabbas ko kungiyar ma’aikatan shari’a ta kasa JUSUN za ta bi sahun kungiyar wajen dakatar da matakin da ta dauka tun farko a jiya kan batun cire tallafin man fetur.