On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ana Saran ASUU Zata Janye Yajin Aikin Watanni Takwas A Ranar Alhamis

ASUU

A ranar Alhamis ne kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU zata yanke hukunci kan janye yajin aikin data shafe watanni takwas tana yi.

An dai ta yada jita-jita a ranar  Litinin dake  cewa  malaman jami’oin sun janye yajin aikin da suke yi, To sai dai wani  daga  cikin ‘yan majalisar gudanarwar kungiyar na kasa, wanda ya bukaci a sakaye sunansa,  Yace har ya zuwa wannan lokaci ba’a janye yajin aikin ba.

Majiyar ta  fadawa manema Labarai  cewa , a  gobe ne kwamitin kolin kungiyar na kasa  zai yi zama na musamman  domin  daukar  matakin da ya dace.

Tun daga ranar  14 ga watan  Fabarairun bana ne, Kungiyar  ta ASUU ta tsunduma yajin aiki a sakamakon abunda ta baiyana na  gazawar gwamnati wajen biya mata bukatunta.