On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ana 'Yar Tankiya Tsakanin Obi Da Gwamnatin Najeriya Kan Zargin Cin Amanar Kasa

‘Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, ya caccaki ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, kan zargin tayar da zaune tsaye bayan zabe.

A wani taron manema labarai da ya yi a birnin Washington DC ranar Talata, Ministan ya gargadi Obi da ya daina rura wutar rikici, bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ministan ya ce, babu yadda Obi da mataimakinsa Datti Ahmed za su ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya barazana kan cewa, muddin aka rantsar da zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a ranar 29 ga watan Mayu, to hakan na nufin kawo karshen demokuradiya.

Sai dai Obi a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Talata, ya yi tir da zarge-zargen da ake yi a lokacin da ake zargin wasu na yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi.

Tsohon gwamnan na Anambra ya bukaci wadanda ya bayyana a matsayin jami’an zarge-zargen karya, da su kauracewa irin haka.