On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Ana Zargin 'Yan Vigilante Da Fasawa Amarya Idanu A Kano

Ana zargin wasu Jami'an Vigilante a unguwar Kwajalawa, ‘Dan-tamashe dake rimin Kebe a karamar hukumar Ungoggo sun fasawa Amarya Idanu yayin da ake tsaka da shagalin bikinta.

Mahaifin amaryar Khadija Abdullahi, Malam Abdu Ma'azu yace bai san hawa ba bai san sauka ba sai ya ji an ce ana rikinci a gidansa, kuma da ya garzaya ya tarar da ‘yan  Vigilante sun tarwatsa  'yan biki, tare da fasa Idon  'Yarsa da ake bikinta.

Daga bisani nan ya garzaya wajen 'yan sanda ya sanar mu su, suka zo suka dauki Khadija zuwa Asibitin Kwararru na Murtala domin duba lafiyarta.

Anata bangaren Amarya Khadija tace suna tsaka da biki sai suka ga Jami'an Vigilante akalla su 10 nan take suka tarwatsa taro, ita kuwa bayan wani duka da akayi ma ta sai ganinta tayi a gadon asibiti.

Mustafa Bala shi ne Angon Khadija yace bai ji dadin abinda ya faru ba na fasawa amaryarsa idanu inda ya yi  fatan za a bi musu hakkinsu.

Da muka tuntubi kwamandan Vigilante na Yankin ya ki cewa komi kan al’amarin, bisa umarnin Mahaifinsa Mai Unguwar kwajalawa.

Kazalika Kakakin Rundunar 'Yan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa yace idan sun tattara bayanai za su sanar da mu halin da ake ciki.

More from Labarai