On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Anyi Garkuwa Da Hakimi Tare Da Wasu Mutane 6 A Zamfara

'Yan ta'adda sun yi garkuwa da hakimin kauyen Kwangami, Muhammad Galadima da wasu mutane shida a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Wani dan asalin yankin  mai suna Dahiru Amadu ya shaidawa manema labarai cewa wasu ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai ne suka yi awon gaba da mutanen a ranar Litinin.

Amadu yace an shiga rudani a kauyen yayin da mazauna yankin ke kokarin tserewa daga harin, inda ya ce mutane da dama sun jikkata.

Ya ce anyi garkuwa da hakimin da sauran mutane shida a cikin gidajensu inda aka kai su sansanin ‘yan ta’adda.