On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

APC TA Lashe Zaben Gwamna A Jihar Ekiti

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti na shekarar 2022.

Mista Oyebanji ya samu kuri’u 187, 57 inda ya kayar da abokan hamayyarsa biyu, Segun Oni na jam’iyyar SDP da Bisi Kolawole na jam’iyyar PDP.

Jam’iyyar SDP ta zo ta biyu da kuri’u  82,211 yayin da PDP ta zo na uku da kuri’u 67,457.

Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar APC ce ta lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar, inda jam'iyyar PDP ta yi nasara a karamar hukuma daya tal.

Sakamakon zaben na nufin Biodun Abayomi Oyebanji zai jagoranci jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa a matsayin gwamna.