On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

ASUU Ta Koka Kan Karancin Malamai A Jami'oi

ASUU

Jami’oin kasar nan na fama da matsalar karancin Ma’aikata, a yayin da dubban malaman manyan makarantun ke haurawa zuwa kasashen waje domin samun aiki mai gwabi, daidai lokacin da masu yin ritaya a jami’oin ke karuwa.

Da dama daga cikin  rassan kungiyar malaman jami’oi  ta kasa  ASUU   sun tabbatar da haka ga jaridar Punch, inda suka alakanta matsalar, da yadda  malaman jami’oin ke  tafiya kasashen waje domin samun aiki, da kuma matsalolin da suka dabaibaye tsarin biyan  albashi  na bai  daya  ga  malaman jami’oi  mai taken IPPIS.

A jami’ar  Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, Kimanin malaman 100  ne suka bar  jami’ar,  ayayin da  jami’ar  gwamnatin tarayya ta Gusau dake zamfara ke bukatar  samun malamai kimanin dubu 1  domin cike  guraben darussan da babu malaman dake koyar  das u.

Haka zalika  kungiyar  ASUU  t ace  a jami’ar koyar da aikin gona  ta Abeokuta dake Ogun, sama da gurabe  350 na malamai ne babu kowa  akansu, a yayin da malamai 27 suka bar   tsangayoyi daban daban  na jami’ar  Legas,  sai  kuma Malamai guda  100  da  suka bar aikin a jami’ar Uyo, inda  suka fice zuwa kasashen waje.

To wannan matsala dai na  zuwa ne a yayin da yanzu haka akwai kimanin kudurorin doka har guda  32, dake gaban zauren majalisar wakilai da kuma  ta Dattawa, dake neman kafa sabbin jami’oi da kwalejojin fasaha da kuma kwalejojin ilimi, tun bayan rantsar da sabon zauren majalisar na  10 da aka yi a bana.

A yanzu haka  akwai jami’oin gwamnatin tarayya guda  52 sai  jami’oin jihohi guda  63  da jami’oi masu zaman kansu guda 147, sai kwalejojin kimiyya da fasaha  na gwamnatin tarayya guda 40, da kuma na jihohi  guda 49, sai kwalejojin  fasaha masu zaman kansu guda 76 da kuma kwalejojin ilimi  har guda  219.

Rahotanni sun baiyana cewar  kakakin majalisar wakilai  na cigaba da matsa lamba  domin ganin a gina sabuwar  Jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayyya  a jihar Kaduna.

Sai dai kungiyar ASUU  da kuma sauran kwararru  a bangaren ilimi  sun gargadi  gwamnati kan kafa  wasu sabbin jami’oin  a yayin da  ta kasa rike  wadanda ake da  su a halin  yanzu.