On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

ASUU Ta Zargi Ministan Kwadago Da Bada Izinin Biyan Malaman Jami'oi Rabin Albashi

EMMANUEL OSODOKE DA NGIGE

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya caccaki ministan kwadago da nagartar aiki, Chris Ngige, bisa zarginsa da ba da izinin biyan rabin albashin watan October ga malaman jami’oi.

Hakan na zuwa ne bayan ASUU a watan Oktoba ta dakatar da yajin aikin data shafe tsawon watanni 8 tana yi bisa ga umarnin da kotun ma’aikata  ta kasa  ta bayar, na cewar  malaman su koma bakin aiki.

Osodeke ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin wata hira da aka yi dashi ta cikin shirin Siyasa a yau  na  gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada cewa, kasancewar   Ngige ya garzaya kotu, ya rasa ‘yancin da yake dashi a  matsayinsa na mai shiga tsakani,  kuma bashi da wani bakin magana akan abunda ke tsakanin kungiyar da gwamnatin taraiyya.

Shugaban  kungiyar ASUU na  kasa ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a warware  matsalolin da kungiyar  ke ciki, domin amfanin dalibai da iyaye dama  kasa baki daya.

Idan za’a iya tunawa, wasu  rassan kungiyar malaman jami’oi ta  ASUU  kamar  UNILAG dake Legas  da Abuja, sun gudanar da zanga-zangar yin  daya dangane da biyansu rabin albashi, A yayin da itama  jami’ar Bayero dake nan Kano zata nuna nata boren a ranar Alhamis mai zuwa.