On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

ASUU Tayi Barazanar Komawa Yajin Aiki

buhari da ASUU

Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU , Ta ce Sabon yajin aiki na barazanar sake kunno kai a jami’oin kasar nan, wanda kuma a halin yanzu matsalar sai ta haura ta lokutan baya da aka fuskanta.

Kungiyar ta yi kira ga ‘yan kishin kasa da sauran masu ruwa da tsaki, dasu  matsawa gwamnatin taraiyya domin ganin ta biya su hakkokinsu na tsawon watanni takwas data rike, domin kaucewa sake  komawa  ‘yar gidan jiya.

Shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar Ilorin, Farfesa  Moyosore Ajao ne yayi wannan barazana a yayin wani taron reshen kungiyar da aka yi, a babban dakin taro na jami’ar.

Ya  ce  duk da kasancewar sun koma bakin aiki, kuma gwamnati tayi shuru abunta kan biyansu hakkokinsu na watanni takwas, a saboda  tsarinta na ba aiki ba biya ,  Babu shakka  zata fuskanci sabon bore na malaman jami’oin.