On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Atiku Abubakar Ya Zabi Gwamna Ifeanyi Na Jihar Delta Amatsayin Abokin Takararsa

'Dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya zabi gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.

Atiku ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a wajen tantance ɗaukar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a shalkwatar jam'iyyar PDP da ke Abuja.

Atiku ya sanar da gwamnan na jihar ta Delta da ke shiyyar kudu maso kudu  Ifeanyi Okowa amatsayin mataimakinsa  bayan shafe kwanaki ana shawarwari da muhawara kan wanda zai tsayar.

Dama an sa ran cewa a ranar Alhamis ɗin ne jam'iyyun siyasa za su sanar da sunayen mutanen da za su zama mataimakan  'yan takararsu na shugaban ƙasa.

A yayin da PDP ta fitar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar , ita kuwa jam'iyyar APC mai mulki na dakon ganin wanda zata tsayar. 

More from Labarai